Isa ga babban shafi
Mali

Mali: An gurfanar da kwamandan kungiyar Ansaruddin a kotun ICC

Kotun hukunci kan manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta bada umarnin ci gaba da tsare Al Hassan Abdoul Aziz Mahmoud, mutumin da ake dade ana nemansa ruwa a jallo, bisa zarginsa da aikata laifukan yaki a Mali.

Wani sashi na birnin Timbuktu da ke kasar Mali.
Wani sashi na birnin Timbuktu da ke kasar Mali. AFP
Talla

Ana zargin AbdoulAziz Mahmoud da yi wa mata da kananan yara matan auren dole da mayakan ‘yan tawaye, a lokacinda ya shugabancin ‘yan sandan mayaka masu da’awar jihadi yayinda suka mamaye birnin Timbuktu, shekaru biyar da suka gabata.

Bayaga taimakawa wajen lalata kayayyakin tarihin da ke birnin, ana kuma zargin madugun ‘yan tawayen da azabtar da fararen hula, aikata fyade, da sauran laifuka na cin zarafin dan adam.

AbdoulAziz Mahmoud zai zama mutum na biyu da kotun ICC zata hukunta bisa aikata laifukan yaki a Mali.

A shekarar 2016, Ahmad al-Faqi al-Mahdi na kungiyar mayakan Ansaruddin ya amince da zarginsa da akai na lalata kayayyakin tarihi masu yawa a mali, tare da rusa wani masallaci a lokacin da suka mamaye birnin Timbuktu tsawon watanni.

Bayan amsa laifinsa ne kotun ICC ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 9, sakamakon barnar da ya tafka na lalata kayayyakin tarihin da darajarsu ta kai kusan dala miliyan 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.