Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Shugabannin Afrika na alhinin mutuwar Winnie Mandela

Shugabannin Kasashen Afrika da fitattun mutanen yankin na ci gaba da bayyana alhininsu da mutuwar Winnie Mandela, tsohuwar matar Nelson Mandela da ta rasu tana da shekaru 81 a jiya Litinin.

Marigayiya Winnie Mandela.
Marigayiya Winnie Mandela. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Cikin wadanda suka bayyana alhininsu da mutuwar har da Arch. Bishop Desmond Tutu, wanda ya ce, Winnie taki bada kai bori ya hau lokacin da aka tsare mijinta a gidan yari na dogon lokaci duk da tirsasawa da tsare ta da kuma korar da jami’an tsaro suka rika yi ma ta.

Sakatare Janar na Jam’iyyar ANC, Ace Magashule, ya ce suna zaman makokin daya daga cikin manyan 'yan Afrika wadda tirjewarta da dagewarta suka karfafa yaki da wariyar launin fata a Afrika ta Kudu da nahiyar baki daya.

Moussa Faki, shugaban gudanarwar Kungiyar Kasashen Afrika, ya ce daukacin iyalan kungiyar sun kadu da mutuwar Winnie Mandela, wadda duniya za ta cigaba da tuna ta a matsayin wadda ta bada gagarumar gudunmawa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana Winnie Mandela a matsayin fitacciyar mata wadda ta jajirce wajen rike fitilar neman 'yanci duk da ukubar da ta shiga bayan tsare mijinta, Nelson Mandela.

Shugaban 'yan adawar Kenya, Raila Odinga, ya ce Winnie ta jagoranci gwagwarmaya mai daci domin tabbatar da cewar, mutanenta sun samu 'yanci.

Winnie ta mutu ne bayan fama da doguwar rashin lafiya, in da ta yi jinya a wani asibiti da ke birnin Johannesburg, kamar yadda kakakinta ya sanar.

TAKAITACCEN TARIHIN WINNIE MANDELA

Nomzamo Winifred Zan-yiwe Winnie Madikizela-Mandela, matar da aka fi sani da Winnie Mandela, ta kasance yar siyasar kasar Afrika ta kudu, mamba a jamíyar ANC mai mulkin kasar, an haife ta ne a ranar 26 Sattumba shekarar 1936 a kasar Afrika ta Kudu kafin ta koma ga mahalicinta a ranar 2 ga watan Afrilun 2018.

Ta zama mata ta 2 ga tsohon shugaban Afrika ta Kudu dattijo marigayi Nelson Mandela daga 1958 zuwa 1996, kafin aurensu ya mutu. Sannan ta haifa wa Nelson Mandela 'ya'ya 4 wato, Zoleka Mandela, Zondwa Mandela, Bambatha Mandela, Zwelabo Mandela-Hlongwane

Winnie Mandela, daya daga cikin fuskokin 'yan gwagwarmayar nuna kyamar wariyar launin fata na tsawon shekaru 25, ta kasance mace da a kullum ke tsaye cikin gwagwarmayar siyasar kasar.

Winnie Mandela na daya daga cikin takwarorinta 'yan gwagwrmaya da suka ci kason Turawan mulkin wariyar jinsi na Apartheid tsakanin 1969 zuwa1970.

Kafin mutuwarta Winnie ta kafa wata jarida da ke wallafa wasikun da ita da mijinta suka rubutawa juna a gidajen kaso da ake tsare da su kafin a sallame ta bayan share tsawon shekaru 7 a daure.

A lokacin da take kaddamar da littafinta da ta rubuta mai sunan kwanaki 421 na zaman wakafi, dan kaso mai lamba 1323/69", ta c,e ta yanke shawarar rubuta littafin ne domin ya zama tarihi ga matasa, hakan kuma zai taimaka wajen kaucewa sake faruwar mummunan bakin mulkin wariyar launin fatar da kasar Afrika ta Kudu ta tsinci kanta a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.