Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Kotu ta yi watsi da karar Winnie Mandela

Kotu a kasar Afirka ta Kudu ta yi watsi da karar da Winnie Mandela tsohuwar matar Nelson Mandela ta shigar a gabanta inda take neman a ba ta gadon gidan marigayin.

Nelson Mandela
Nelson Mandela AFP/Daniel Janin
Talla

Kotun wadda ta yi zama a garin Mathatha da ke Lardin Cap, ta ce gidan Mandela da ke garinsa na asali Qunu, ba mallakin Winnie ba ne, hukuncin da ya kawo karshen ja-ja-injar da ake yi tsakanin ‘yan uwan na Nelson Mandela.

Nelson Mandela ya shafe mafi yawa daga cikin kuruciyarsa a Qunu, bayan haihuwarsa, kuma koda bayan ya yi ritaya yana yawaita kai ziyara garin, kazalika a garin aka bine shi bayan mutuwarsa a shekarar 2013.

A Wasiyar da marigayin ya bari, ya damka ragamar gidansa a hannu iyalansa, sai dai Madikizela Mandela tsohuwar matar shi, ta dage kan cewa mallakarta ne gidan karkashin dokar tsarin ma’aurata, saboda an siya gidane kafin su rabu a shekarar 1989.

Mandela ya aure Winnie Madikizela ne a shekarar 1956 kana sun rabu a shekarar 1996.

A wata sanarwar da suka fitar iyalan Mandela sun bayana farin cikinsu da wannan hukunci, inda suke cewa yanzu zasu samu kwanciyar hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.