Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

An yi bukin addu'o'i ga marigayi Nelson Mandela

Dubban mutane daga ciki, da wajen kasar Afrika ta kudu suka hade da shugabannin wasu kasashen duniya fiye da 80, a yau talata a dandalin wasanni na birnin Soweto, domin halatar addu’o’i na musamman domin girmama gawar tsohon shuganan kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela, yayin da wasu milyoyin mutanen, za su kalli jana’izar ta akwatunan Talibijin a sassa daban daban na duniya.Taron jana’izar ya hada shugabanin kasashen da ke adawa da juna a wuri guda, duk domin karama marigayi Mandela wanda jigo ne na fafutukar samun yanci a Afirka ta Kudu.A cikin shugabanin da za su yi jawabi a wannan jana’izar sun hada da shugaban Amurka Barack Obama da na Cuba Raul Castro da kuma Dilma Rousef ta Brazil haka zalika da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Kin MoonShugaban kwammitin da ke kula da shirye shiryen jana’izar Clayson Monyela ya bayyana yanayin da kasar take ciki da cewar kamar karbar bakuncin al’ummar duniya baki daya ne, inda ya kara da cewa ba ya jin an taba samun taro irin wannan a duniyaSai dai duk da wadanan hidimar akwai wasu shugabanni da suka ce ba za su hallara ba saboda wasu dalilai. Wadannan sun hada da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya ce ba zai halarci jana’izar ba saboda da rashin kudi, yayin da aka ce wani aminin Mandela wato Dalai Lama shugaban masu gwagwarmaya na yankin Tibet ba zai samu damar hallarta ba sanadiyar rashin takardar izinin shiga kasar, wati Visa.Sai dai a Turkiya ministan wasannin kasar ne ya gargadi hukumar kwallon kafa ta kasar, wadda ta yi barazanar korar wasu ‘yan wasa da ke kasar wato Didier Drogba da Emmanuel Eboue, saboda sun sanya riguna da ke dauke da rubuta kalamai da ke jinjinawa marigayi Mandela a filin wasa. 

Taron masu addu'ar Nelson Mandela a Africa ta Kudu
Taron masu addu'ar Nelson Mandela a Africa ta Kudu REUTERS/Yves Herman
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.