Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

An binne Mandela a kauyen Qunu

An binne Nelson Mandela shugaba bakar fata na farko a kasar Afrika ta Kudu a kauyen Qunu inda ya girma a gabashin lardin Cape. Kafin binne tsohon shugaban a yau ranar Lahadi, mutanen kasar sun zubar da hawaye tare da yin alkawalin bin tafarkin koyarwar Mandela ta gaskiya da adalci.

Manyan Hafsoshin Sojin Afrika ta Kudu suna girmama gawar Nelson Mandela da aka binne a kauyen Qunu inda ya girma. Mandela ya mutu ne a ranar 5 ga watan Disemba 2013.
Manyan Hafsoshin Sojin Afrika ta Kudu suna girmama gawar Nelson Mandela da aka binne a kauyen Qunu inda ya girma. Mandela ya mutu ne a ranar 5 ga watan Disemba 2013. REUTERS/SABC via Reuters
Talla

An binne Mandela ne a gaban matarsa Graca Machel, da tsohuwar matarsa Winnie Madikizela-Mandela da sauran dangi da kuma manyan baki sama da 450.

Akwai jawabi na girmamawa da bankwana da shugabannin kasar Afrika ta kudu suka gabatar akan marigayi Nelson Mandela gwarzon da ya kawo karshen wariya launin fata a kasar.

“Mutumin da aka binne anan shi ne mafi girma a kasar Afrika ta Kudu” a cewar mataimakin shugaban kasa Cyril Ramaphosa.

Hafsoshin Soji ne suka dauki akwatin gawar Mandela zuwa makwancin shi a Qunu inda daruruwan mutanen kauyen suka yi masa bankwana.

Akwai abokan Mandela da suka yi fafutika tare da suka halarci bikin Jana’izar shi da suka hada da George Bizos da Desmond Tutu da Ahmed Kathrada wanda suka yi zaman kaso tare.

“Na hadu da Mandela shekaru 67 da suka gabata, inji Kathrada wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai a gidan yari tare da Mandela a 1963.

Mista Kathrada ya gabatar da jawabin girmamawa ga Mandela wanda ya kira “mai fafutikar kwato ‘yanci”.

An kwashe kwanaki 10 mutanen Afrika ta kudu suna juyayin mutuwar tsohon shugabansu wanda ya mutu a ranar 5 ga watan Disemba.

A lokacin da ya ke gabatar da Jawabi shugaban kasa Jacob Zuma yace Afrika ta kudu zata ci gaba da rayuwa karkashin makarantar Mandela tare da kira ga mutanen kasar su rungumi dabi’un Mandela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.