Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Akwatin Gawar Mandela ya isa Pretoria Fadar Gwamnati

Akwatin gawar Nelson Mandela ta isa birnin Pretoria, fadar Gwamnatin Afrika ta kudu inda Gawar zata kwashe tsawon kwanaki uku kafin a binne tsohon shugaban na Afrika ta kudu. Tuni dubban mutanen Afrika ta kudu da shugabannin duniya suka gudanar da Addu’oi tare da girmama Mandela a filin wasa na Soweto.

Manyan hafsoshin Sojin kasar Afrika ta kudu suna dauke da gawar Nelson Mandela zuwa Fadar Gwamnati a Pretoria
Manyan hafsoshin Sojin kasar Afrika ta kudu suna dauke da gawar Nelson Mandela zuwa Fadar Gwamnati a Pretoria REUTERS/Kim Ludbrook/Pool
Talla

An dauki gawar Mandela ne daga dakin aje gawawwaki a Asibiti, inda za'a aje gawarsa a ginin Fadar shugaban kasa har tsawon kwanaki uku.

Shugaban Amurka Barack Obama shi ne ya jagoranci tawagar shugabannin duniya a taron girmama Nelson Mandela tare da dubun dubatar mutanen Afrika ta Kudu a babban filin wasa na Soweto da aka gudanar da gasar cin kofin Duniya.

A lokacin da ya ke jawabi, Mista Obama yace an yi babban rashi tare da yin habaici ga shugabanni masu mulkin danniya wadanda ke ikirarin za su yi koyi da Nelson Mandela.

A jiya Talata ne shugabannin kasashen duniya suka halarci taron share fagen jana’izar tsohon Shugaban kasar Afrika ta kudu, Nelson Mandela, taron da har ila yau dubban mutane daga sassa daban daban na duniya suka halarta.

Sai dai duk da cewa batun jana’izar shi ne kan gaba, amma a daya bangaren, taron ya bai wa wasu shugabannin kasashen da ke hamayya da juna damar da suka sha hannu da junansu yayin da wasu suka zauna tare da juna.

Kasar Amurka ta kwashe fiye da shekaru 50 ta na sa-in-sa da kasar Cuba, lamarin da ya sa Amurka ta kakabawa kasar Cuba jerin takunkumi tare da sa kafar wando daya da tsohon shugaba Fidel Castro, wanda kanninsa Raul Castor ke shugabancin kasar a yanzu.

A jiya Talata miliyoyin mutane a sassa daban daban na duniya sun yi sheda da idanunsu, wasu ta akwatunan Talibijinsu, inda aka kafa wani tarihi yayin da shugaba Barack Obama ya sha hannu da Raul Castro.

Obama shi ya fara mikawa Castro hanu yayin da ya nufi dandalin da zai gabatar da jawabinsa akan Madiba, lamarin da wasu ke ganin dabi’a ce da Mandela ya koyar ta yafe wa juna.

A wani yanayi makamancin wannan, tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, ya isa taron ne tare da shugaba mai ci Francois Hollande yayin da Tsoffin Firaministocin Birtaniya da suka hada da John Major da Tony Blair da Gordon Brown da ke da banbancin ra’ayi suka taru a karkashin rumfa daya.

Masu sharhi a duniya da dama, na ganin wannan ita ce irin dabi’ar da Madiba ya koyar ta nuna kauna ga juna duk da akwai banbance banbancen ra’ayi tsakanin shugabanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.