Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Shekara guda da mutuwar Mandela

Gwamnatin kasar Afrika ta kudu za ta jagoranci zaman makoki a bikin cika shekara guda da mutuwar tsohon shugaban kasar Nelson Mandela. Al’ummar kasar za su fito su tsaya na tsawon wani lokaci a ranar 5 ga watan Disemba da Mandela ya mutu.

Marigayi Nelson Mandela Tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu.
Marigayi Nelson Mandela Tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu. © AP Photos
Talla

Za a kada karaurawa da mabusar Vuvuzela na tsawon minti uku da dakikoki bakwai domin juyayin Mandela.

Cibiyar Nelson Mandela ta bukaci makarantun kasar da kungiyoyin al’umma su fito domin bikin tuna Mandela, wanda ya kawo karshen nuna wariyar launin fata a kasar.

Akwai wasannin Cricket da Rugby da za a gudanar domin Mandela, inda tuni Afrika ta kudu ta doke Cote d’Ivoire ci 2 da 0 a wasan kwallon kafa na sada zumunci da suka fafata domin karrama Tsohun shugaban kasar Afrika ta kudu.

Mandela ya rasu yana da shekaru 95 a duniya, bayan ya kwashe watanni yana jinya a asibiti.

Mandela ne bakar fata na farko da ya shugabanci Afrika ta kudu a shekara ta 1994 bayan da ya kwashe shekaru 27 a gidan kurkuku saboda tsayawa da ya yi tsayin daka na ganin an kawo karshen mulki wariyar launan fata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.