Isa ga babban shafi
Najeriya

Zan sake tsayawa takara ne saboda bukatar 'yan Najeriya - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai tsaya takara ne don neman zagaye na biyu a mulkin kasar bisa bukatar da al'ummarsa suka mika masa ta neman hakan.

Sanar da Aniyar Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari na zuwa a dai dai lokacin da ya ke ci gaba da shan suka musamman daga bangaren babbar jam'iyar adawar kasar PDP dama wani bangare na mambobin jam'iyyarsa ta PDP.
Sanar da Aniyar Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari na zuwa a dai dai lokacin da ya ke ci gaba da shan suka musamman daga bangaren babbar jam'iyar adawar kasar PDP dama wani bangare na mambobin jam'iyyarsa ta PDP. REUTERS /Stringer
Talla

Wata Sanarwa da Mataimakin Shugaban na Musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar ta ce dubban al'ummar Najeriyar sun nuna bukatar ganin shugaban ya zarce zuwa zagaye na biyu, matakin da ya tilasta shi amincewa da hakan don ci gaba da aikin farfado da kasar daga halin da ta fada.

Sanarwar wadda Garba Shehu ya fitar na zuwa ne jim kadan bayan furta aniyar sake tsayawa takarar da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya yi a wajen taron jam'iyyarsa ta APC da ya gudana a Abuja babban birnin Kasar.

Wannan ne dai karon farko Muhammadu Buhari ke sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takarar mulkin Najeriyar a bainar jama’a ko da ya ke dai a baya ya sha nuna alamun da ke nuna cewa shugaban na da burin neman wa’adi na biyu akan karagar mulki.

Sanar da Aniyar Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari na zuwa a dai dai lokacin da ya ke ci gaba da shan suka musamman daga bangaren babbar jam'iyar adawar kasar PDP dama wani bangare na mambobin jam'iyyarsa ta PDP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.