Isa ga babban shafi
wasanni

Super Eagles ta dawo ta 6 a iya kwallo a Afrika

Najeriya ta daga sama da akalla mataki biyar a jadawalin da FIFA ke fitarwa kowanne wata kan kasashen da suka fi iya kwallo a Duniya.Yanzu haka dai Najeriyar ita ce ta 47 a duniya kuma ta Shidda a Afrika da akalla maki 635.

Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles.
Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles. Reuters/Peter Cziborra
Talla

A jadawalin da ya gabata kafin na yau Najeriyar ita ke a matsayin ta 52 a jerin kasashen da suka fi iya kwallo da maki 609.

A nahiyar Afrika Tunisia ce a kololuwa kuma ta 14 a duniya sai kuma kasashen Senegal da Jamhuriyar Dimocradiyyar Congo da ke mara mata baya a matsayin na 28 da 38 a duniya.

A duniya baki daya kuma Jamus ce ke ci gaba da rike kambunta a matsayinta daya sai kuma Brazil ta biyu yayinda Belgium wadda a baya ke matsayin ta 5 yanzu ta dawo ta 3.

A ranar 17 ga watan Mayu mai zuwa ne Fifar zata kara fitar da wani jadawalin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.