Isa ga babban shafi
Najeriya

Super Eagles ta koma ta 10 a iya kwallo a Afrika

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta fado zuwa mataki na 51 a jadawalin kasashen da suka fi iya murza kwallo a duniya cikin rahoton da hukumar kwallon kafa ta duniya ta fitar yau dinnan. Haka zalika, FIFA ta bayyana cewa yanzu Najeriyar ita ce ta 9 a jerin kasashen da suka fi iya kwallo a Nahiyar Afrika.

Tawagar kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles yayin wani atisaye kafin tunkarar wasanni.
Tawagar kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles yayin wani atisaye kafin tunkarar wasanni. AFP/Javier Soriano
Talla

Rahoton ya nuna cewa Ghana ce ta dare kan matakin Najeriyar na baya yayin da yanzu take mataki na 8 na jerin kassahen da suka fi iya kwallo a Nahiyar Afrika.

Jadawalin kasashen na Nahiyar Afrika ya nuna cewa yanzu Senegal ce ta daya kuma ta 23 a duniya sai Tunisiya wadda ke matsayin ta 2 kuma a mataki na 27 a duniya yayinda Masar ke matsayin ta 3 kuma ta 3.

Rahoton ya nuna cewa yanzu Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ce ta 4 kuma ta 39 a duniya yayinda Morocco ke biye mata baya a matsayi na 5 kuma na 40 a duniya.

Sauran kasashen sun hada da Burkinafaso mai mataki na 6 kuma 44 a duniya kana Kamaru a mataki na 7 kuma na 45 sai Ghana ta 8 kuma ta 50 a duniya yayinda Najeriya ke mataki na 51 kuma na 9 a Afrika sai kuma ta karshe wato Aljeriya da ke mataki na 10 kuma na 58 a duniya.

Har ila yau Jadawalin na FIFA ya nuna cewa har yanzu kasashen Jamus da Brazil da kuma Portugal su ke rike da matakan ukun farko na kasashen da suka fi iya kwallon kafa a Duniya.

Hukumar ta FIFA ta ce akwai dan ci gaba ga kasashen Argentina da Belgium wadanda yanzu ke mataki na 4 dana biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.