Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun tare hanyar Maiduguri zuwa Kano

Rahotanni daga garin Maidurin jihar Borno na cewa wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan boko haram ne sun tare babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Kawo yanzu dai babu tabbacin ko jami'an tsaro sun tunkare su ko akasin haka, haka zalika babu labarin adadin mutanen da suka hallaka.
Kawo yanzu dai babu tabbacin ko jami'an tsaro sun tunkare su ko akasin haka, haka zalika babu labarin adadin mutanen da suka hallaka. REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Majiyoyin labarai na cewa an tarin motocin matafiya na ta juyawa inda suka fito a dai dai garin Auno wanda bashi da nisa da shiga garin Maiduguri.

Majiyoyin na cewa 'yan bindigar na ta barin wuta a dai dai garin na Auno.

Babu dai wasu bayanai na irin asarar da aka tafka ya zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.