Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta yi suka kan shirin samar da Makiyayu na Gwamnatin Najeriya

Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta yi kakkausar suka ga matakin gwamantin kasar game da shirin samar da makiyayu na zamani har 94 a jihohin kasar 10.Sukar ta PDP na zuwa ne kwana guda bayan gwamnatin Najeriyar karkashin Muhammadu Buhari ta sanar da gina Makiyayun zamani ga Makiyayan kasar don kawo karshen rikicin da ake fuskanta tsakaninsu da Manoma.

A baya dai Jam'iyyar ta PDP na daga cikin bangarorin da ke matsa kaimi ga gwamnatin ta Muhammadu Buhari wajen ganin ta samar da mafita ga rikicin na Makiyaya da Manoma.
A baya dai Jam'iyyar ta PDP na daga cikin bangarorin da ke matsa kaimi ga gwamnatin ta Muhammadu Buhari wajen ganin ta samar da mafita ga rikicin na Makiyaya da Manoma. Sarah Elzas
Talla

Jam’iyyar ta PDP ta bakin sakatarenta na kasa Mr Kola Ologbondiyan ya ce da alamu gwamnatin na kokarin rura wutar rikicin na makiyaya da manoma maimakon daukar matakin kawo karshensa.

Mr Kola kamata ya yi gwamnatin ta tuntube wadanda ke da masaniya kan batun ba wai yanke mataki kai tsaye da nufin da’da’dawa wani bangare ba, wanda ya ce matakin zai iya kaiwa ga haddasa rikici.

A cewarsa rashin daukar matakin tuntubar wadanda ke da masaniya kan batu, shi ke kara jefa gwamnatin mai ci a rikici, inda a ya ce rikicin ka iya zarce na koyaushe matukar gwamnatin bata yi taka tsan-tsan ba, musamman da yake batu ne daya shafi kabilanci.

Jam’iyyar ta PDP ta kuma bukaci gwamnatin da ta girmama tanadin da kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 199 ya yi kan batun da ya shafi makiyayu.

A baya dai Jam'iyyar ta PDP na daga cikin bangarorin da ke matsa kaimi ga gwamnatin ta Muhammadu Buhari wajen ganin ta samar da mafita ga rikicin na Makiyaya da Manoma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.