Isa ga babban shafi
Mali

Al'ummar Mali na kada kuri'a zaben shugaban kasa zagaye na biyu

Al’ummar Mali sun soma kada kuri’a a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu, tsakanin shugaba Ibrahim Boubacar Keita da abokin hamayyarsa kuma tsohon ministan kudin kasar Souma’ila Cisse.

Wasu 'yan kasar Mali a birnin Bamako, yayin dakon jefa kuri'unsu a zaben shugabancin kasar. 29, Yuli, 2018.
Wasu 'yan kasar Mali a birnin Bamako, yayin dakon jefa kuri'unsu a zaben shugabancin kasar. 29, Yuli, 2018. REUTERS/Luc Gnago
Talla

A zagayen farko na zaben, da aka yi a watan da ya gabata, shugaba Kieta ne ke kan gaba, bayan lashe kashi 41 na kuri'un  da aka kada, yayinda Cisse ya samu kashi 18.

Sai dai kafin zaben na yau, a jiya Asabar, jami’an tsaron kasar ta Mali, sun bayyana samun nasarar wargaza wani shirin kaddamar da hare-haren ta’adanci a sassan Bamako babban birnin kasar, inda suka kame mutane 3.

Akalla jami’an sojin kasar dubu 36,000 ake sa ran zasu samar da tsaro a sassan kasar, yayin da zaben ke gudana, inda za’a sa ido sosai kan yankin Mopti da ke tsakiyar kasar, inda a yanzu yafi fuskantar barazanar hare-hare da barkewar rikici.

Wasu daga jami’an sa ido kan zaben na Mali sun ce, yayin gudanar da zagayen farko na zaben shugabancin kasar, tashe tashen hankula sun tilasta rufe akalla kashi daya daga cikin biyar, na rumfunan zabe, a sassan kasar.

Zaben na Mali ya zo ne a daidai lokacin da sojoji ke fafutukar murkushe hare-haren ta’addanci da kuma rikicin kabilanci a sassan kasar, musamman a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar.

Har yanzu dai Faransa na da dakaru dubu 4,500 a Mali, wadanda ke aiki da rundunar wanzar da zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya mai dakaru 15,000 da kuma rundunar hadin gwiwar kasashe biyar ta G5 Sahel, domin dawo da cikakken tsaro a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.