Isa ga babban shafi
Mali

Keita ya lashe zaben Mali da gagarumin rinjaye

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Kieta yayi nasarar lashe zaben shugabancin kasar zagaye na biyu da gagarumin rinjaye akan abokin hamayyarsa Souma’ila Cisse.

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita
Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita REUTERS/Luc Gnago
Talla

Sakamakon da hukumar zaben kasar ta Mali ya nuna cewa shugaba mai ci Ibrahim Boubacar Keita ya samu kashi 67 na kuri’un da aka kada, yayinda Souma’ila Cisse ya samu kashi 32.8 na kuri’un da aka kada a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata, 12 ga watan Agusta, 2018.

A zagayen farko na zaben da ya gudana a ranar 29 ga watan Yuli, Keita ne ya fi samun kuri’u da sama da kashi 41 cikin 100, yayinda Souma’ila Cisse ya samu kashi 17 cikin 100. Rashin samun dan takarar da ya lashe kuri’u kashi 50 a zagayen farko ne ya sabbaba kaiwa ga zagaye na biyu.

Kididdiga ta nuna cewa kashi 34.5 na al’ummar kasar ta Mali ne suka samu fitowa kada kuri’unsu a zagayen zaben na biyu.

Zaben dai ya gudana ne cikin zargin cewa gwamnati za ta tafka magudi daga bangaren ‘yan adawa, lamarin da yasa tun a ranar Litinin da ta gabata, babban abokin hamayyar Keita a zaben, Souma’ila Cisse shan alwashin yin watsi da sakamakon zaben.

A ranar 4 ga watan Satumba mai zuwa ake sa ran Ibrahim Boubacar Keita mai shekaru 73 zai karbi rantsuwar kama aikin wa’adi na biyu, cike da fatan zai karfafa yarjejeniyar sulhun da gwamnati ta cimma da tsaffin ‘yan tawayen Azibinawa a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.