Isa ga babban shafi
Sudan-Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi gurfanar da Omar al-Bashir a ICC

Kwamitin kare hakkin bil’adam na Majalisar Dinkin Duniya ya nemi lallai a gurfanar da jami’an tsaron gwamnatin kasar Sudan da ke da hannu wajen barnar da aka yi cikin kasar tsakanin shekara ta 2014 da shekara ta 2016.

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir.
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Bayanan da Kwamiti ya gabatar na cewa akwai bukatar Gwamnatin Sudan ta bada hadin kai ga kotun hukuntan manyan laifuka ta duniya ICC wadda ta bukaci a kamo mata Shugaban Sudan Omar Al-Bashir saboda laifukan yaki.

Kwamitin na nanata cewa al’amarin kisan masu laifuka wajen ratayesu ko jefesu da Hukumomin kasar ke yi da kuma wulakanta ‘yan jaridu da masu ra'ayi mabanbanta da na Gwamnati sam basu dace ba.

Dubban mutane ne dai aka kashe a yakin kasar ta Sudan, da kuma yankin yammacin Darfur inda ‘yan tawaye suka jaa daaga suna fafatawa da Sojan Gwamnati, lokacin da gwamnatin ta kara waadin dokar ta baci.

Kwamitin na nuna rashin jin dadi yadda Gwamnatin Sudan ta ki gurfanar da kowa game da manyan laifukan da aka yi a cikin kasar, dama aiwatar da umarnin kotun ta ICC da ke bukatar a kamo mata manyan jami'an Gwamnati da ake zargi suna da hannu.

Shugaban Sudan Omar al-Bashir dai ya sha musanta bashi da hannu wajen laifukan yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.