Isa ga babban shafi
Najeriya-Abuja

An gudanar da Jana'izar Janar Alkali a Abuja

Rundunar Sojin Najeriya ta gudanar da sallar Jana’iza ga Babban Jami’inta Manjo Janar Idris Alkali yau Asabar a babban masallacin kasar da ke birnin Abuja, bayan gano gawarsa ranar Laraba cikin wata tsohuwar rijiya ta Guchwet da ke yankin Shen a karamar hukumar Jos ta kudu da ke jihar Filato a Najeriya.

An dai yi amfani da Tutar Najeriyar wajen rufe gawar mamacin wanda ke nuna martaba a matsayinsa na wanda ya rasa ransa yana tsaka da hidimtawa kasar.
An dai yi amfani da Tutar Najeriyar wajen rufe gawar mamacin wanda ke nuna martaba a matsayinsa na wanda ya rasa ransa yana tsaka da hidimtawa kasar. rfihausa
Talla

Sallar Jana'izar wadda ta gudana karkashin jagorancin Hafson sojojin Najeriyar Laftanar Janar Yusuf Tukur Burutai ta samu halartar manyan jami'an soji kasar iyalan jami'in da wasu jami'an gwamnati da dai daikun jama'a.

An dai yi amfani da Tutar Najeriyar wajen rufe gawar mamacin wanda ke nuna martaba a matsayinsa na wanda ya rasa ransa yana tsaka da hidimtawa kasar.

Tun a ranar 3 ga watan Satumban da ya gabata ne aka fara neman Janar Alkali wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja kuma aka kuma daina samun wayarsa a dai dai lokacin da ya isa yankin kudancin Jos cikin motarsa mai lambar Kwara MUN 670 AA, yayinda aka gano motar ta sa daga bisani gabanin gano gawarshi dungurumum.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.