Dakarun Faransa a Mali sun kashe mayakan jihadi
Rundunar Faransa a kasar Mali ta sanar da kai wasu samame kan ayarin wasu mayakan jihadi a arewacin kasar daga daren Alhamis zuwa jiya juma’a.Sanarwar da Minstar tsaron Faransa Florence Parly ta sanyawa hannu tareda bayyana cewa Faransa ta yi amfani da manyan jiragen yaki, jirage masu saukar ungulu.
Wallafawa ranar:
Samamen da Dakarun Faransa suka kai ya kai su ga samun nasarar murkushe mayakan jihadi da dama, daga cikin su ana yi zana Hamadoun Kouffa mataimakin daya daga cikin Shugabanin kungiyoyin yan tawayen arewacin Mali Iyag Ag Ghali .
Akalla Faransa ta girke kusan soji 4.500 a yankin Sahel, rundunar dake taimakawa wajen yaki da yan ta’ada a yankin na Sahel.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu