Isa ga babban shafi
Amurka-Najeriya

Najeriya ta bukaci Amurka ta hana Atiku izinin shiga kasar

Gwamnatin Najeriya ta shaidawa Amurka cewar kar ta bai wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar bizar zuwa kasar, domin yin haka zai nuna cewar ta na goyan bayan takarar sa ne a zaben shekara mai zuwa.

A cewar gwamnatin Najeriyar bayar da izinin ga Atiku yana matsayin mara baya ne ga takararsa ta neman shugabancin kasar.
A cewar gwamnatin Najeriyar bayar da izinin ga Atiku yana matsayin mara baya ne ga takararsa ta neman shugabancin kasar. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Ministan yada labaran Najeriyar Lai Mohammed wanda ke wanann batu a Abuja ya ke suna da labarin yunkurin da Atiku ke yi na ganin Amurka ta cire masa takunkumin shiga kasar.

Ministan ya ce duk da yake Amurkar ce ke da ikon bada bizar ga wanda ta so, bai wa Atikun a halin yanzu zai nunawa jama’a cewar ta na goyan bayan takarar da ya ke yi.

Atiku Abubakar ya dade yana bayyana cewar ya nemi izinin zuwa Amurka a baya, amma ba’a ba shi biza ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.