Isa ga babban shafi
Najeriya

Malaman jami'o'in Najeriya sun sha alwashin ci gaba da yajin aiki

Malaman Jami’oi a Najeriya sun ce za su ci gaba da yajin aikin da suke yi har sai gwamnati ta biya musu baki dayan bukatun da suka gabatar mata.

Wasu daga cikin malaman jami'o'in Najeriya, dake nuna bacin rai kan rashin baiwa jami''o'in isassun kudaden gudanarwa.
Wasu daga cikin malaman jami'o'in Najeriya, dake nuna bacin rai kan rashin baiwa jami''o'in isassun kudaden gudanarwa. Daily Post
Talla

Shugaban malaman jami’o’in Biodun Ogunyemi, yace sun gana da Ministan ilimi amma har yanzu babu wata matsaya da aka cimma, saboda haka zasu cigaba da yajin aikin.

Mista Ogunyemi ya koka bisa cewar a halin da ake ciki, jami’o’in Najeriya basa iya jan hankulan manyan malamai daga kasashen ketare da ma dalibai zuwa garesu, wanda hakan zai taimaka sosai wajen daga darajar jami’o’in na Najeriya a idanun duniya.

Daya daga cikin manyan dalilan da suka sanya kungiyar malaman jami'o'in ta ASUU tsunduma yajin aikin shi ne rashin baiwa makarantun jami'o'in na Najeriya isassun kudaden da suke bukata wajen inganta ayyukansu na yau da kullum da suka hada da gyrawa da gina karin wuraren daukar karatu da kuma samar da isassun kayan aiki.

Matakin malaman jami’o’in na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kwadago ke cigaba da tauna tsakuwa kan bukatar karin albashin da take nema, wanda a baya da shiga yajin aikin gama gari wanda gwamnati shawo kanta ta janye shi daga bisani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.