Isa ga babban shafi
Najeriya

An ci gaba da zabe a wasu yankunan Zamfara

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta ce yau Lahadi an kada kuri’u a sassan wasu jihohin kasar da ba a samu damar yin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisunsa ba a jiya Asabar.Jihohin da lamarin ya shafa a cewar INEC, sun hada da Zamfara, Jigawa da kuma Benue.

Hukumar zaben Najeriya ta samu isa da kayan zabe zuwa wasu yankunan kasar da aka samu tsaiko
Hukumar zaben Najeriya ta samu isa da kayan zabe zuwa wasu yankunan kasar da aka samu tsaiko REUTERS/Tife Owolabi
Talla

An kammala zabukan a Zamfara a rumfunan zabe 77 da ke kananan hukumomin jihar 10, kamar yadda jami’in yada labaran hukumar INEC reshen jihar Garba Galadima ya tabbatar.

Galadima ya danganta rashin yin zaben kamar yadda aka tsara a jiya da matsalolin, rashin tsaro, samun tangardar na’ura da kuma rashin isar kayan aiki da wuri.

A wani labarin mai alaka da wannan, kwamishinan hukumar zaben Najeriya na jihar Benue, Nentawe Goshwe, ya ce, yau Lahadi an sake zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisunsa, a wasu rumfunan zabe 5 da ke kananan hukumomin jihar uku.

Kananan hukumomin sun hada da Oturkpo, Apa da kuma Ogbadibo.

Kwamishinan zaben na jihar ta Benue, ya ce tangardar na’urar tantance masu kada kuri’a ta card reader ta haddasa tsaiko wajen gudanar da zabukan kamar yadda aka tsara a ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.