Isa ga babban shafi
Algeria

Dalibai sun shiga zanga-zangar adawa da tazarcen Bouteflika

Dubban dalibai a Algeria sun kauracewa makarantunsu inda suka shiga zanga-zanga mafi girma da aka taba gani a kasar cikin shekaru da dama, wadda aka soma ta a makon da ya gabata don nuna adawa da aniyar tazarcen shugaba AbdelAziz Bouteflika.

Dubban masu zanga-zanga a Algeria, da ke neman kawo karshen mulkin shugaban kasar AbdelAziz Bouteflika.
Dubban masu zanga-zanga a Algeria, da ke neman kawo karshen mulkin shugaban kasar AbdelAziz Bouteflika. RYAD KRAMDI / AFP
Talla

Karfin zanga-zangar ya karu ne, jim kadan bayan tayin da shugaba Bouteflika ya yiwa ‘yan kasar na su sake zabar shi wa’adi na 5, shi kuma yayi alkawarin sauka bayan shekara daya.

Sai dai a maimakon tayin ya kwantar da hankula sai ya sake harzuka dubban ‘yan kasar, da suke ci gaba fita zanga-zangar kawo karsen mulkin Bouteflika na tsawon shekaru 20.

A shekarar 1999 AbdelAziz Bouteflika mai shekaru 82 a yanzu, ya dare kujerar shugabancin Algeria, amma a shekarar 2013 ya rage fita cikin jama’a, bayan kamuwa da ciwon mutuwar barin jiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.