Isa ga babban shafi
Algeria

Dubban 'yan Algeria sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga

Dubban al’ummar Algeria sun sha alwashin ci gaba da yin zanga-zanga, har sai sun karasa cimma burin sauya tsari da alkibilar siyasar kasar, duk da cewa sun yi nasarar kawo karshen mulkin shekaru 20 na shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika.

Dubban 'yan Algeria a birnin Algiers.
Dubban 'yan Algeria a birnin Algiers. REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

A ranar Talata shugaba Bouteflika mai shekaru 82, ya mika takardarsa ta yin murabus, bayan shafe makwanni, yana fuskantar zanga-zangar dubban ‘yan kasar da ke neman yayi Murabus.

Sai dai bayan murabus din Bouteflika, dubban ‘yan kasar sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga har sai sun tilasta saukar manyan mukarrabansa, da kuma yiwa tsarin siyasar kasar garambawul.

An dai soma zanga-zangar adawa da shugabancin Bouteflika makwanni 6 da suka gabata, bayanda shugaban ya bayyana aniyar neman wa’adi na 5 a babban zaben kasar da a baya aka tsara zai gudana a ranar 18 ga watan Afrilu.

Daga bisani, ya janye aniyarsa, amma da sharadin dage zabukan kasar zuwa wani lokaci da bai bayyana ba. Sai dai Matakin ya sake tunzara masu zanga-zangar wadda dubban dalibai da malamansu da kuma manyan lauyoyi suka karawa karfi.

Tuni dai tsohon shugaban na Algeria Abdelaziz Bouteflika ya nemi gafarar ‘yan kasar cikin wasikar da ya rubuta ta ajiye mukamin kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.