Isa ga babban shafi
Afrika

Tsohon Shugaban Benin ,Boni Yayi ya gargadi Shugaba Talon

Tsohon Shugaban Jamhuriyar Benin Boni Yayi ya gana da manema labaren kasashen Duniya domin sanar da su halin da kasar sa ke ciki da kuma bayyana takaicin sa ga salon siyasar Shugaban kasar mai ci Patrice Talon.

Zanga-zangar yan adawa a Jamhuriyar Benin
Zanga-zangar yan adawa a Jamhuriyar Benin Yanick Folly / AFP
Talla

Ranar 28 ga watan Afrilun nan ne za a gudanar da zaben yan Majalisu ,wanda ga baki daya hukumar zaben kasar ta soke takardun jam’iyoyi masu adawa da Shugaban kasar.

Wannan lamari ya soma haifar da tashin hankali a wasu sassan kasar musaman arewacin kasar Benin.

Shugaban kasar Patrice Talon a baya, ya bayyana cewa ya yi iyakacin kokarin sa don gani an shawo kan wannan matsalla ,sai dai bangaren yan adawa sun kaucewa zaman tattaunawa na kawo karshen rikicin da ya kuno kai tsakanin su.

Tsohon Shugaban kasar Boni Yayi ya bayyana damuwa matuka da cewa yanayin siyasa da kasar ta fada zai iya haifar da tashin hankali mudin Shugaban kasar Patrice Talon bai dau matakan da suka dace don baiwa yan adawa damar shiga zaben kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.