Isa ga babban shafi
Afrika

Yan Shi'a sun yin kokarin kutsa kai cikin majalisar Najeriya

A yau Laraba mabiya akidar Shi’a sun yi kokarin kutsa kai cikin majalisar dokokin kasar dake Abuja.Zanga-zangar dake gudana don nuna bacin ran su ga ci gaba da tsare Shugaban su Ibrahim El-Zakzaky, da ake yi yanzu haka.

Mabiya Shi'a a Najeriya
Mabiya Shi'a a Najeriya Reuters
Talla

Mataimakin Shugaban Majalisa a zaman yan majalisu na yau Laraba Yusuf Lasun ya sheidawa manema labarai cewa ,wakilan jama’a majalisar sun dakatar da zaman su a lokacin da mabiya shi’a suka yi kokarin cire babbar kofar majalisar.

Idan aka yi tuni a yan watanni da suka gabata, kungiyar Amnesty International a wata sanarwa da ta fitar,ta ce ga alama, Sojojin Najeriya na amfani da wasu dabaru da aka kitsa da gan-gan don kashe ‘Yan Shi’a a yayin taronsu.

A cewar sanarwar, binciken Amnesty ya nuna cewa, Sojoji da Jami’an ‘Yan sanda da suka yi amfani da karfin da ya wuce kima sun kashe ‘Yan Shi’a akalla 45 a cikin kwanaki biyu.

Amnesty ta ce, Jami’anta sun halarci wurare daban-daban guda biyar a Abuja da jihar Nasarawa don ganawa da mabiya Shi’ar da ke karbar magani sakamakon raunin da suka samu a tashin hankalin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.