Isa ga babban shafi
Najeriya-Human Right Watch

Human Right Watch ta bukaci hukunta sojin Najeriya kan kisan 'yan Shi'a

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch ta bukaci hukunta sojojin Najeriya da suka yi amfani da karfi wajen kisan mabiya Shi’a fiye da 300 tun bayan fara takaddamarsu shekaru 3 da suka gabata a mabanbantan zanga-zanga.

Kungiyar ta kare hakkin dan adam ta ce akalla ‘yan Shi’a 40 jami’an tsaron Najeriya suka hallaka cikin kwanaki 3 da suka yi suna zanga-zanga a Abuja babban birnin kasar.
Kungiyar ta kare hakkin dan adam ta ce akalla ‘yan Shi’a 40 jami’an tsaron Najeriya suka hallaka cikin kwanaki 3 da suka yi suna zanga-zanga a Abuja babban birnin kasar. REUTERS/Abraham Achirga
Talla

A cewar kungiyar ta Human Right watch sojin Najeriyar sun yi amfani da karfi wajen kisan gilla ga mabiyan na Shi’a baya ga kame wasu tare da daure su, ba bisa ka’ida ba, yayinda gwamnati ta yi kememe ba tare da daukar matakan da suka dace ba, batun da kungiyar ta Human Right watch ke cewa babbar barazana ce ga tsaron kasar.

Kungiyar ta kare hakkin dan adam ta ce akalla ‘yan Shi’a 40 jami’an tsaron Najeriya suka hallaka cikin kwanaki 3 da suka yi suna zanga-zanga a Abuja babban birnin kasar, yayinda ma’aikatar tsaron kasar ta ce mutane 6 ne kacal suka mutu.

Aniete Ewang, jami’in kungiyar da ke jagorantar bincike kan rikicin ‘yan shi’ar da jami’an tsaron Najeriyar, ya ce a lokuta da dama Sojin kan yi amfani da karfin tuwo ne wajen kwace makaman da ke hannun mabiyan tare da hallaka wasu baya kame da dam aba kuma tare da bayar hujjar yin hakan ba, a inda bangaren shari’ar kasar kuma ya gaza daukar matakin da ya kamata.

A cewar Jami’in ci gaban rikicin tsakanin ‘yan shi’a da jami’an tsaro na nuna yadda bangaren shari’ar Najeriyar ya gaza wajen yin adalci kan wadanda ake zalunta, bugu da kari kuma hakan ke nuna yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.