Isa ga babban shafi
Afrika

Ana tsare da wasu magoya bayan Kamto a Kamaru

A Kamaru akalla magoya bayan dan adawa Maurice Kamto da ya kasance na biyu a zaben Shugabancin kasar 300 ne aka kama bayan kazamar zanga-zanga da ta gudana a wasu biranen kasar ta Kamaru.

Maurice Kamto,jagoran yan adawa a kasar Kamaru
Maurice Kamto,jagoran yan adawa a kasar Kamaru RFI/Capture d'écran
Talla

Magatakardar jam’iyyar MRC ta dan adawa Maurice Kamto ya bayyana wasu biranen kasar da suka hada da Yaounde , Douala, Bafoussam da Nkongsamba inda aka yi ta kama magoya bayan su, daga ciki harda mataimakin shugaban jam’iyyar Mamadou Mota.

Ya zuwa hukumomin Kamaru basu ce upon ba dangane da batun tsare wasu magoya bayan jam’iyyar adawa da a yan Sanda ke yi yanzu haka, yayinda lauyoyin dake kare jam’iyyar adawa suka aike da wasika zuwa majalisar dimkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.