Isa ga babban shafi
DR Congo-Ebola

An sake buda iyakar da ta hada kasashen Congo da Rwanda

An sake buda iyakar da ta hada kasashen Congo da Rwanda ta bangaren biranen Goma da Gisenyi, awowi 8 bayan da aka bayyana rufeta, sakamakon sake gano bulluwar cutar Ebola a yankin mai karfin tattalinarziki ta fannin kasuwanci dake gabashin jamhuriyar demokradiyar Congo, kamar yadda wata sanarwar fadar shugabancin kasar jamhuriyar demokradiyar Congo ta sanar.

An sake samun tum na 3 dauke da kwayar annobar Ebola a Goma, 31 yuli 2019.
An sake samun tum na 3 dauke da kwayar annobar Ebola a Goma, 31 yuli 2019. PAMELA TULIZO / AFP
Talla

Yanzu dai al’ummomin bangarorin biyu, sun sake koma wa hada hadar kasuwanci da kai kawo a tsakaninsu kamar yadda aka saba a biranen na Goma da Gisenyi.

Dafarko dai wata sanarwar fadar shugaban kasar rwanda, ce ta bayyana daukar mataki ya haramtawa yan kasar fita zuwa Goma a Jamhuriyar Demokradiyar Congo

A karkashin wannan sabon mataki dai yan kasar ta Congo na iya barin Gisenyi dake Rwanda zuwa Goma bangaren Jamhuriyar Demokradiyar Congo, sai dai ba za a bari su sake dawowa kasar ta Rwanda ba, domin hanabazuwaar annobar ta Ebola da tuni ta yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 1.800 a shekra guda a kasar ta Jamhuriyar Demokradiyar Congo. Matakin da kasar ta Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta yi tir da shi,

Rufe bodar da mahukumtan Rwanda suka yi kan yan kasar ta Congo da ma baki dake rayuwa a Gisenyi, da a kullum suke kai kawo a Goma, ya saba wa ka’idojin hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya kan yancin shige da ficen jamaá a yanki, a cewar fadar shugabancin kasar ta Congo

Amma kuma an baiwa yan kasar ta Kongon damar tsallaka iyakar su shiga Goma sai dai babu zancen dawowa a Rwanda, har ma da wadanda ke rayuwa a Gisenyi da iyalansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.