Isa ga babban shafi

Sojin Algeria ta bukaci 'yan sanda su kame masu shirin zanga-zanga

Rundunar Sojin Algeria ta bukaci jami’an 'yan Sanda su tare masu futowa daga sassan kasar domin shiga birnin Algiers da zummar shiga zanga zangar adawa da gwamnati da kuma bukatar korar wasu jami’ai kafin gudanar da zaben shugaban kasa.

Wata mace tsaye gaban dan sanda Algeria da ke lura da masu zanga-zanga
Wata mace tsaye gaban dan sanda Algeria da ke lura da masu zanga-zanga AFP
Talla

Janar Ahmed Gaid Salah, shugaban rundunar sojin kasar ta Algeria ya sanar da bai wa 'yan Sandan umarnin ladabtar da duk masu zuwa zanga zangar ba tare da tausayawa ba.

Janar Salah ya ce daukar matakin na da muhimmanci domin hana masu wata mummunar aniya biyan bukatar su.

Shugaban riko Abdelkadir Bensalah ya sanar da ranar 12 ga watan Disamba mai zuwa a mastayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa, sai dai wasu tsirarun al'ummar kasar na son kawar da wasu manyan jami'an gwamnati gabanin zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.