Isa ga babban shafi
Algeria

Kotun fasalta tsarin mulkin Algeria ta dage zaben shugaban kasa

Kotun fasalta kundin tsarin mulkin Algeria ta ce zaben shugabancin kasar ba zai gudana a lokacin da aka tsara ba, a ranar 4 ga watan Yuli.

Wasu 'yan Algeria yayin zanga-zanga dauke da tutar kasar a birnin Algiers. 31/5/2019.
Wasu 'yan Algeria yayin zanga-zanga dauke da tutar kasar a birnin Algiers. 31/5/2019. AFP/Ryad Kramdi
Talla

Sanarwar da kotun ta fitar a Yau Lahadi ta kara tsawaita lokacin kafa sabuwar gwamnati a kasar ta Algeria, watanni biyu, bayan murabus din da tsohon shugaban kasar AbdelAziz Bouteflika yayi,bayan shafe shekaru 20 yana mulki.

Kotun fasalta kundin tsarin mulkin ta Algeria ta ce, matsar da lokacin zaben zuwa gaba ya zama tilas, saboda rashin ‘yan takarar da suka cancanta, la’akari da cewa dukkanin ‘yan takarar shugabancin kasar guda 2 da suka fito, basu cika ka’idojin da ake bukata ba.

Matsin lambar tilastawa tsohon shugaba Bouteflika yin murabus ya soma ne bayanda ya bayyana aniyar neman wa’adi na 5 a babban zaben kasar da a baya aka tsara zai gudana a ranar 18 ga watan Afrilu.

Bayan zafafar zanga-zangar dubban ‘yan Algeria, Bouteflika ya janye aniyarsa ta neman tazarce, amma da sharadin dage zabukan kasar zuwa wani lokaci da bai bayyana ba.

Matakin shugaban na Algeria ya sake tunzara masu zanga-zangar wadda dubban dalibai da malamansu da kuma manyan lauyoyi suka shiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.