Isa ga babban shafi
Afrika

Yan Adawa a Haiti na kalubalantar Shugaba Jovenel Moise

Kasar Haiti ta shiga wani halin rashin tabbas ta fuskar siyasa, kasancewa wa’addin yan Majalisun kasar ya kawo karshe.Yan adawa na cigaba da sa mantsin lamba ga Shugaban kasar Jovenel Moise, wanda ya bayyana cewa shirya zabukan yan majalisu nauyi ne da yake kan Gwamnatin kasar, sai dai rashin kuddaden da suka dace ba shi baiwa gwamnatin kasar damar shirya zaben kasar.

Jovenel Moise, Shugaban kasar Haiti a wani bikin tuni da mutanen da suka rasa rayukan su a girgizar kasa a Haiti
Jovenel Moise, Shugaban kasar Haiti a wani bikin tuni da mutanen da suka rasa rayukan su a girgizar kasa a Haiti REUTERS/Andres Martinez Casares
Talla

Rashin gudanar da zabukan yan Majlisu da na kananan hukumomi a watan Nuwamban shekarar da ta shude na dada nuna gazawar gwamnatin Shugaba Jovenel Moise na dimke barraka ganin mauyacin hali da yan kasar suka fada.

Yan adawa na ci gaba da kira don ganin Shugaban kasar yayi murabis, yan adawa na tabbatar da cewa suna da sheidu dake gaskanta cewa Shugaban kasar na da hannu a batutuwan da suka jibanci cin hantsi.

A daya geffen Sakatary majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres a wata wasika da ya aike zuwa gwamnatin Haiti, ya gayyace su da su kaucewa tada tarzoma da kan iya haifar da wani sabon rikici zai jeffa kasar cikin wani yanayi na rashin tabbas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.