Girgizar kasa ta kashe mutane 11 a Haiti
An sami girgizan kasa mai karfi a Haiti wadda ta kai maki 5.9 a ma’auninta inda ta kashe mutane akalla 11 da lalata gidaje masu yawan gaske.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kakakin Gwamnatin kasar Eddy Jackson Alexis ya fadawa manema labarai cewa cikin mamatan guda bakwai sun mutu ne a garin Port-de-Paix yayin da mutane hudu sun gamu da ajalinsu ne a garin Gros-Morne mai tazaran kilomita 50 ta shiyyar kudu maso gabashin kasar.
Kamar yadda Hukumar dake Kula da harkokin jama’a ta sanar akwai mutane 135 da suka jikkata.
Girgizan kasar ta yi barna a garuruwan Chansolme da tsubirin Tortuga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu