Isa ga babban shafi

kwamandan Amurka ya zargi Turai da gazawa a Sahel

Kwamandan Rundunar Sojin Amurka dake kula da Afirka, Janar Stephen Townsend ya yi zargin cewar kokarin kasashen Turai na yaki da ‘yan ta’adda a Yankin Sahel bashi da tsari da kuma tasiri, kuma wannan ya hana su samun nasara.

Sojin Faransa a yankin Sahel
Sojin Faransa a yankin Sahel Reuters
Talla

Yayin da yake tsokaci kan bukatar sanya hannun Amurka cikin yakin a gaban wani kwamitin Yan Majalisu, Janar Townsend ya bukaci Karin kokari daga bangaren kasashen Turan kafin Amurka ta shigo ta kuma taka rawa a Yankin.

Janar Townsend yace akwai tarin taimakon soji dake zuwa Yankin daga kasashen Turai da kuma hadin kan Faransa da Turai da Amurka, amma saboda rashin tsari mai kyau a gaza cimma nasara.

Hafsan sojin ya bayyana Yan ta’addan dake Yankin Sahel a matsayin babbar barazana ga Turai, a maimakon Amurka duk da fargabar da Majalisar wakilai keyi.

Mataimakiyar Sakataren tsaron Amurka dake kula da Turai da Afirka, Kathryn Whewlbarger tace sun shaidawa Faransa matsalar, lokacin da ta bukaci Amurka ta taimaka da kwarewar da basu da ita.

Wheelbarger tace suna iya bakin kokarin su wajen karfafawa Turai gwuiwa ta hanyar daukar matsayi a lokacin da ya dace domin rage dogaro da Amurka.

Faransa na da dakaru 5,100 a karkashin rundunar Barkhane dake yaki da Yan ta’adda a Afirka, yayin da take bukatar Amurka ta sanya hannu wajen samun nasarar yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.