Isa ga babban shafi
Mali

Duk da Covid-19 mutanen Mali na zaben 'yan majalisa a wannan lahadi

Yayin da kasashen duniya ke daukar matakai don hana taruwar jama’a a wannan lokaci da ake yaki da cutar coronavirus, a yau lahadi a’ummar kasar Mali na gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki zagaye na biyu.

Malamin zabe sanye da takunkumi a garin Gao, ranar 29, marsi 2020. (image d'illustration) Souleymane Ag Anara / AFP
Malamin zabe sanye da takunkumi a garin Gao, ranar 29, marsi 2020. (image d'illustration) Souleymane Ag Anara / AFP AFP
Talla

A karshen watan jiya ne aka gudanar da zagayen farko na wannan zabe, to sai dai an samu karancin fitowar jama’a, abin da ya sa da kyar aka zabi ‘yan majalisa 22 daga cikin 147 da ke zauren majalisar dokokin kasar.

Wasu daga cikin dalilan da suka haddasa karancin fitowar jama’a a zaben na farko sun hada da bullar annobar Coronavirus da kuma rashin tsaro a yankin tsakiya da arewacin kasar.

Yanzu haka jagoran ‘yan adawar kasar Soumaila Cisse, daya daga cikin ‘yan takarar a wannan zabe na ci gaba da kasancewa a hannun ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da shi lokacin da yake yakin neman zabe a ranar 25 ga watan maris da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.