Isa ga babban shafi
Morocco

Morocco ta dawo da harkokin yau da kullum bayan nasarar yakar coronavirus

Morocco ta sanar da shirin dawo da hada-hadar jiragen sama daga ranar 24 ga watan nan na Yuni bayan da ta kammala janye dokar killace jama’a da ta gindaya a baya don yaki da cutar COVID-19.

Bayan janye ilahirin dokokin hana taruwar jama'a da aka dauka watanni baya don yakar cutar coronavirus.
Bayan janye ilahirin dokokin hana taruwar jama'a da aka dauka watanni baya don yakar cutar coronavirus. REUTERS/Manaure Quintero/File Photo
Talla

Sanarwar gwamnatin kasar a safiyar yau Lahadi ta ce hatta gidajen cin abinci, gidajen rawa da sauran wuraren taruwar jama’a za su dawo bakin aiki sai dai za su rage yawan mutanen da ke haduwa, in banda a yankunan Tangier da Larache da Marrakech da kuma Kenitra yankunan da cutar ta fi tsananta a kasar, wadanda gwamnatin ta ce za su ci gaba da fuskantar haramcin taruwar jama’a amma suma babu sauran dokar kulle.

Sanarwar ta ce hada-hadar jirage a iya cikin kasar za su koma kamar yadda su ke haka zalika jigilar jiragen kasa, sai dai ta ce har yanzu masallatai da makarantu za su ci gba da kasancewa a kulle wala’Alla zuwa 10 ga watan Yuli ko Satumba.

Yanzu haka dai Morocco na da yawan masu dauke da cutar ta COVID-19 dubu 9 da 957 ciki kuwa har da matattu 213 sai kuma mutum dubu 8 da 249.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.