Fada ya barke tsakanin kungiyoyin fasakwauri a Sahel
Rahotanni daga Agadez da ke Jamhuriyar Nijar sun ce wani fada da ya barke tsakanin kungiyoyin da ke safarar makamai da kwayoyi a kusa da iyakar Libya da Algeriya ya yi sanadiyar rasa dimbin rayuka.
Wallafawa ranar:
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewar tsakanin Alhamis da juma’ar da suka gabata, an samu fafatawa tsakanin kungiyoyin da ke safara a yankin inda aka kashe mutane sama da dozin guda.
Wani jami’in yankin Agadez ya ce daya daga cikin bangaren kungiyoyin ne ya yi kwantan bauna inda ya kai hari ga dayan a kokarin mamaye safarar makamai da kwayar da ake yi a yankin.
Wata majiya ta ce mutanen da aka kashe sun kai 17 daga bangarorin biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu