Emmanuel Macron zai halarci taron shugabannin kasashen G5 Sahel
Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai halarci taron shugabannin kasashen G5 Sahel dake yaki da Yan ta’adda wanda za’a gudanar da shi a Mauritania a makon gobe, a daidai lokacin da ake cigaba da samun karin hare hare daga Yan ta’addan.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce hare haren Yan ta’adda da kuma rikicin kabilanci sun zama ruwan dare a Yankin abinda ke kai ga rasa dimbin rayuka.
Tashe-tashen hankulla a tsakiyyar kasar Mali, dake fama da hare haren mayakan jihadi, rikici tsakanin kabilu da kuma wuce gona da irin da jami’án tsaro ke yi, sun yi sanadiyar mutuwar mutane 508 daga watan janairu zuwa yau.
Ana saran taron na ranar talata ya kunshi shugabanin kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Nijar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu