Isa ga babban shafi
Sahel

Kasashen G5 Sahel za su yi taron gaggawa a Yamai

Gwamnatocin Mali da Nijar sun ce ranar lahadi taron shugabannin kasashen G5 Sahel zai gudana a birnin Yamai, domin tattaunawa kan matakan tsaro a yankin, biyo bayan kazamin harin da mayaka masu ikirarin jihadi suka kai kan barikin sojin Inates, inda suka kashe dakarun Nijar 71.

Hedikwatar rundunar hadin gwiwa ta G5 Sahel a Sevare dake Mali.
Hedikwatar rundunar hadin gwiwa ta G5 Sahel a Sevare dake Mali. AFP / Sebastien Rieussec
Talla

Ranar lahadin ne dai Nijar za ta karkare makokin kwanaki 3 na dakarun nata da suka kwanta dama a farmakin da aka kaiwa sansaninsu dake yammacin kasar.

Harin na ranar talata 10 ga watan Disambar 2019, shi ne mafi muni da mayaka masu ikirarin jihadi suka kaiwa dakarun Nijar, farmakin da mayakan IS suka dauki alhaki.

A baya bayan nan dai mayakan sun takura wajen kai kazaman hare-hare a yankin Sahel, musamman kan Burkina Faso, sai kuma Nijar, duk da karfafa rundunar hadin gwiwar kasashe biyar na G5 Sahel, gami da taimakon dakarun Barkhane na Faransa akalla dubu 4 da 500, da kuma wasu dakarun Amurka.

A halin yanzu kasar Burkina Faso ke jagorantar hadin gwiwar kasashen na G5 Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.