Isa ga babban shafi
Mali

Jonathan ya fara aikin sasanta rikicin Mali

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya isa birnin Bamako na Mali, inda  ya fara aikin da kungiyar ECOWAS ta ba shi na shiga tsakani a rikicin gwamnatin kasar da ‘yan adawa da zummar lalubo mafita.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kasar Mali ta tsunduma cikin rikici sakamakon zanga-zangar kira ga shugaba Ibrahim Boubacar Keïta da ya yi murabus, inda tarzoma ta barke a zanga-zangar baya-bayan nan sakamakon dirar mikiyar  da jami’an tsaro suka yi wa masu boren.

Tuni Jonathan ya gana da shugaba Keita jim kadan da saukarsa birnin Bamako a ranar Laraba.

Kungiyar ECOWAS ce ta nada tsohon shugaban na Najeriya a matsayin shugaban tawagar sansantawa da za ta shiga tsakani a madadinta a rikicin na Mali.

Kafofin yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa tsohon shugaba Jonathan ya samu goyon-baya daga shugaba Muhammadu Buhari wanda ya tanadar masa da jirgin sama da sauran abubuwan da yake bukata don saukaka masa tafiyar.

Jirgin saman samfuri Gulfstream 550 jet, mallakin gwamnatin Najeriya da ya dauki tsohon shugaban na Najeriya, ya tashi daga birnin Abuja tare da yada zango a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar, kafin ya karasa birnin Bamako.

Ana sa ran kwararru a fannin tsarin mulki daga kasashen Benin da Togo da Cote d’Ivoire za su kasance a wannan tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.