Isa ga babban shafi

Human Rights Watch ta zargi sojojin Mali da kissan Masu zanga-zanga

Hukumar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta zargi jami’an tsaron Mali da amfani da karfi fiye da kima kan masu zanga zangar kin jinin gwamnati.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a kasar Mali
Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a kasar Mali AP Photo/Baba Ahmed
Talla

Zanga zangar adawa da shugaba Ibrahim Boubacar Keita ta rikide zuwa tarzoma a ranar 10 ga watan Yuli, inda jami’an tsaro da masu zanga zanga suka kwashe kwanaki 3 suna kai ruwa rana.

Kungiyar kare hakkiin bil adamar ta ce mutane 14 ne suka mutu a tarzomar, yayin da 300 suka jikkata, amma jam’iyyar adawa ta ce mutane 23 ne suka mutu.

Kungiyar Amnesty International ma ta yi makamaicin wannan zargi a baya, inda ta zargi jami’an tsaron gwamnati da hannu wajen amfani da karfin da ya wuce kima da ya kai ga kashe masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Mali a watan jiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.