Isa ga babban shafi
Mali

Ana fargabar juyin mulkin soji a Mali

Ana fargabar juyin mulki bayan an jiyo harbe-harben bindiga a babban sassanin soji da ke kusa da birnin Bamako na Mali a wannan Talata, kamar yadda shaidu da jami’an tsaro suka bayyana.

Sojojin Mali sun yi bore tare da harbe-harben bindiga a sassanin Kati mai nisan kilomita 15 daga babban birnin Bamako.
Sojojin Mali sun yi bore tare da harbe-harben bindiga a sassanin Kati mai nisan kilomita 15 daga babban birnin Bamako. AFP PHOTO / PHILIPPE DESMAZES
Talla

Babu dai cikakken bayani game da wannan al’amari, amma majiyoyi sun bayyana cewa, sojoji sun yi harbi a iska a sansanin da ke garin Kati mai nisan kilomita 15 daga birnin Bamako.

Wani jami’in tsaro da ke sansanin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, harbe-harben bindigar na da nasaba da bore kuma akasarin sojoji ba sa farin ciki da halin da siyasar Mali ke ciki.

Jami’in ya kara da cewa, suna bukatar sauyi.

Lamarin dai ya yi daidai da shirin ‘yan adawa na dawo da zanga-zangar kyamatar shugaba Ibrahim Boubacar Keita.

Sansanin sojin Soundiata Keita da ke garin Kati na karkashin ikon sojoji kuma suna da makamai da dakaru da kuma kayayyakin yaki.

Sai dai fusatattun sojojin sun karbe iko da hatta hanyoyin da suka ratsa zuwa birnin Bamako mai tazarar kilomita 15 daga garin na Kati.

Wani likiti a garin Kati ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, akwai sojoji da dama kuma suna cikin hali na fusata.

Tuni wasu ma’aikatan gidan rediyo da talabijin na ORTM mallakin gwamnati suka wuce gidajensu, yayin da wasu ma’aikatan suka fice daga cikin gine-ginen hukumomi.

Kawo yanzu gwamnatin Mali ba ta ce uffam ba game da wannan al’amari, yayin da ake sa ran nan da ‘yan sa’o’i kalilan a samu cikakken bayani.

Boren kifar da gwamnati da aka yi a shekarar 2012 da ya yassare wa shugaba Keita darewa kan karagar mulki, ya taso ne daga wannan sansani na garin Kati, abin da ya sa a yanzu ake fargabar cewa, harbe-harben ka iya zama wani sabon yunkurin juyin mulki a raunanniyar kasar.

Sai dai Amurka na adawa haramtaccen sauyin da ya saba wa kundin tsarin mulki a Mali kamar yadda jakadanta na musamman a yankin Sahel, J. Peter Pham ya bayyana a wannan Talata.

Ita ma Faransa da ta yi wa Mali mulkin mallaka, ta shawarci kowa da kowa da ya zauna a gida a wani sako da ofishin jakadancinta ya wallafa a shafukan sada zumunta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.