Isa ga babban shafi
Morocco

Morocco ta musanta jita-jitar kulla hulda da Isra'ila

Gwamnatin Morocco ta yi watsi da rahotannin da ke bayyana cewar ta kulla yarjejeniyar hulda da Isra'ila wadda ke cigaba da zawarcin kasashen larabawa.

Sarkin Morocco Muhammad na VI.
Sarkin Morocco Muhammad na VI. Reuters/Jamil Bittar
Talla

Firaministan kasar Saad Dine El Otmani ya ce babu dalilin da za su kulla hulda da kasar da ke cigaba da take hakkin Falasdinawa.

Kalaman Firaministan na zuwa ne a daidai lokacin da Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da Jared Kushner, sirikin Donald Trump da ke jagorancin sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya ke fara ziyarar yankin.

Kasar Morocco da Israila sun fara kwarya kwarya hulda a shekarar 1993 bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa amma sai Morocco ta soke huldar a shekara ta 2000 bayan rikicin da ya barke tsakanin Israila da Falasdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.