Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 65 a Nijar

Ambaliyar ruwa ta yi mummunar barna a kasashe da dama na yammacin Afirka, da suka hada da Senega da Najeriya da Nijar da kuma Burkina Faso.A jamhuriyar Nijar kadai, mahukunta sun ce an samu asarar rayukan mutane 65 a bana, yayin da mutane sama da dubu 300 suka rasa muhallansu.

Wani yanki na Yamai da ambaliya ta mamaye
Wani yanki na Yamai da ambaliya ta mamaye BOUREIMA HAMA / AFP
Talla

A jamhuriyar Nijar din, sakamakon da ya gabata ya nuna cewa mutane 45 ne suka mutu wasu dubu 226. Suka rasa mahallansu

Yanayin ambaliyar ruwan da ta shafi daukacin kasar daga ranar 7 ga watan September 2020 ya nuna cewa mutane dubu 329.958 ne suka rasa mahallansu dake wakiltar iylai dubu 38.099.

An samu mutane 51 da suka mutu sanadiyar gine ginen gidajen da suka afka a kansu, 14 sun mutu ne ta hanyar nutsewa a yayinda wasu 90 suka jikkata kamar yadda ofishin ministan dake kula da ayukan jinkai da kuma kai dauki ga Iftalaí ya sanar

Baya ga gidaje, da bukoki dubu 34.000 da suka ruguje ambaliyar ruwan saman ta mamaye filayen noma da aka kiyasta cewa ya kai murabaín Eka dubu 5.768.

Wani sakamakon da aka bayar ya bayyana rushewar azuzuwan karatu sama da 60 masalatai sama da 20 tare da rumbunan adana abinci 448 gda kuma rijiyoyin ruwan sha 713.

Yankunan da matsalar ta fi shafa sun hada ne da Maradi (dake tsakiya masu kudancin kasar), sai Tahoua da Tillabéri (dake yammaci), Dosso (kudu maso yammaci) da kuma birnin Niamey, shima yankin arewaci dake cikin sahara bai tsira ba daga iftlaín na ambaliyar ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.