Jigawa: Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 20, gidaje dubu 50 sun rushe
Hukumar bada agajin gaggawa ta Jigawa dake arewacin Najeriya, tace yawan mutanen da ambaliyar ruwa ta halaka a jihar ya kai 20, yayinda kuma ta rusa dubban gidaje gami da lalata tarin amfanin gona.
Wallafawa ranar:
Yayin karin bayani ga manema labarai a garin Dutse, sakataren hukumar agajin gaggawar Yusuf Sani Babura, yace ambaliyar ruwan ta shafi kananan hukumomi 17 daga cikin jumilar 27 dake jihar.
Yanzu haka dai dubban jama’ar da iftila’in ya shafa na tsungune a makarantu, masallatai da wasu gidajen jama’ar da suka basu mafakar wucin gadi.
Kididdigar hukumar bada agajin gaggawar ta Jigawa ta nuna cewar akalla gidaje dubu 50 ambaliyar ruwa ta rusa, yayinda kuma ta shafe gonaki masu yawan gaske da suka hada da na, masara, gero, dawa da kuma shinkafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu