Isa ga babban shafi
Botswana

Cuta ce ke kashe giwaye a Botswana ba mafarauta ba- Gwamnati

Gwamnatin Botswana ta ce wata cuta ce da ke da nasaba da guba ta yi sanadiyyar hallaka daruruwan giwayen da suka mutu a Gandun dajin Okavango Delta, sabanin zargin da ake yiwa masu farautar giwayen domin sayar da hauren su.

An dai fara samun rahotan mutuwar giwayen ne a ranar 25 ga watan Afrilu a kusa da kauyen Seronga
An dai fara samun rahotan mutuwar giwayen ne a ranar 25 ga watan Afrilu a kusa da kauyen Seronga TONY KARUMBA / AFP
Talla

Hukumar dake kula da gandun dajin Botswana ta sanar da cewar mutuwar da akalla giwaye sama da 300 suka yi a gandun dajin tsakanin watan Maris zuwa yanzu bashi da nasaba da masu kashe giwayen domin cire hauren su.

Mmadi Reuben, Babban likitan dake kula da ma’aikatar gandun dajin ya ce wata cuta da ake kira ‘cynobacteria’ da turanci da ake samu a ruwan da baya gudu ya yi sanadiyar mutuwar tarin giwayen, kafin ayi nasarar dakile cutar a karshen watan Yuni.

An dai fara samun rahotan mutuwar giwayen ne a ranar 25 ga watan Afrilu a kusa da kauyen Seronga, kuma sannu a hankali adadin yayi ta karuwa.

Hukumomin kula da gandun dajin sun ce akalla dabbobin 330 suka mutu, kuma gwajin kimiya da aka yi a kasashen Afirka ta kudu da Canada da Zimbabwe da kuma Amurka sun tabbatar da abinda ya hallaka su.

Kasar Botswana ce kasar da tafi yawan giwaye a duniya, inda ta ke da akalla 130,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.