Isa ga babban shafi
Duniya-Sahel

Majalisar Dinkin Duniya ta shirya gidauniyar taimakawa kasashen Sahel

Majalisar Dinkin Duniya ta shirya kaddamar da gidauniyar tara kudaden da za’a taimakawa kasashen Sahel wadanda rikice rikice da sauyin yanayi da kuma annobar korona ta jefa miliyoyin mutanen su cikin halin yunwa.

Taswirar yankin Sahel
Taswirar yankin Sahel Ministère français des Affaires étrangères
Talla

Kasar Denmark ta shirya gidauniyar tare da Jamus da kungiyar kasashen Turai da kuma Majalisar da zummar kara kaimi wajen janyo hankalin masu karfin fada aji a duniya kan halin da ake ciki a yankin.

Kakakin hukumar jinkai ta Majalisar Jens Laerke yace mutanen dake zama a kusa da iyakokin Mali da Burkina Faso da Nijar na fuskantar matukar tashin hankali da talauci da kuma sauyin yanayi, abinda ya sa ya zama wajibi a taimaka musu domin kaucewa zama daya daga cikin yankunan da ake fuskantar bala’i a duniya.

Jami’in yace ya zuwa yanzu ana samun kasha 40 ne kawai na kudaden da ake bukata domin gudanar da aikin jinkai a yankin mai dauke da mutane sama da miliyan 13 dake bukatar agajin gaggawa.

Majalisar tace mutane sama da miliyan guda da rabi sun rasa matsugunan su a yankin, wanda yawan su ya ribanya har sau 20 kan yadda ake da su a shekaru 2 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.