Isa ga babban shafi
Afrika

Weah yace ba zai cigaba da zama a karagar mulki ba

Shugaban kasar Liberia George Weah yace ba zai cigaba da zama a karagar mulki ba bayan kamala wa’adin sa biyu, a wani yunkuri na kawar da rade radin da ake cewar zai nemi yin wa’adi na 3.

George Weah Shugaban kasar Liberia
George Weah Shugaban kasar Liberia JACK GUEZ / AFP
Talla

Yayin da yake ganawa da manema labarai a Monrovia, Babban Hafsa a Fadar shugaban kasa, Nathaniel McGill yace Weah da bai kamala wa’adin sa na farko ba, baya tunanin sauya kundin tsarin mulkin kasar domin cigaba da zama a karaga.

McGill yace ba tsari mai kyau bane mutum guda ya cigaba da zama a matsayin shugaban kasa na dogon lokaci, saboda haka babu gaskiya a ciki.

Yanzu haka ana cigaba da cece kuce a cikin kasar cewar, shugaban mai shekaru 54 zai bi sahun wasu takwarorin sa na Afirka wajen sauya kundin tsarin mulkin domin cigaba da zama a karaga.

Wannan ya biyo bayan abinda aka gani a kasashen Guinea da Cote d’Ivoire inda shugaba Alpha Conde da Alassane Ouattara suka sauya kundin kasashen su.

Ana saran mutanen Liberia su kada kuri’ar raba gardama domin yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.