Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa na nazarin rage sojojin ta dake yaki a sahel

Kasar Faransa na nazarin rage sojojin ta dake yaki da Yan ta’adda a Yankin sahel kasa da shekara guda bayan tura Karin daruruwa domin tabbatar da tsaro a Yankin.

Sojojin Faransa na Barkhane a arewaci Mali
Sojojin Faransa na Barkhane a arewaci Mali AFP Photo/MICHELE CATTANI
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Jean Yves Le Drian da ministar tsaro Florence Parly sun ziyarci kasar Mali a yan makwannin da suka gabata domin taimakawa gwamnati nazarin halin da sojojin kasar ke ciki a yankin Sahel da kuma Yankin dake kudu da Sahara tun bayan girke su a shekarar 2014 a karkashin rundunar Barkhane.

Yayin ziyarar Mali, Parly ta ce ganin an kama hanayr zuwa karshen wannan shekara, lokaci yayi da za’ayi nazarin halin da dakarun ke ciki da kuma aikin da suke yi, bayan da shugaba Emmanuel Macron ya bayyana cewar zasu sake fasalin rundunar ta Barkhane.

Majiyoyi sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar gwamnati ta shirya janye daruruwan sojoji daga rundunar ta Barkhane wadda yanzu haka ke da dakaru 5,100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.