Kamaru ta daure matar da ta bukaci a yi wa gwamnati bore
Kotun Soji a Kamaru ta daure shugabar reshen mata na babbar jam’iyyar adawar kasar ta MRC, Fri Awasum Mispa watanni 6 a gidan yari saboda samun ta da laifin tinzira jama’a da su gudanar da boren kifar da gwamnati.
Wallafawa ranar:
An dai kama Mispa ce a ranar Asabar da ta gabata a birnin Yaounde tare da wasu mata akalla 20 da suka shiga gangami domin ganin an saki shugabansu Maurice Kamto.
Kotun ta ce ana iya sake tsawaita hukuncin daurin watanni 6 bayan karewarsa.
Kamto a karshen mako ya zargi gwamnatin Paul Biya da yunkurin tarwatsa jam’iyyarsa da kuma hana su gudanar da ayyukan siyasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu