Isa ga babban shafi

Amurka ta soma amfani da sabon taswirar kasar Morocco da ya kunshi yankin Polisario

Algeria ta yi Allah - Wadai da katsalandan din kasashen ketare kan makomar yankin Polisario wadanda tace sun kulla aniyar haddasa tashin hankali a yankin da ma kasashen dake makwabtaka da shi.

Sojojin yankin Polisario na Morocco yayin fareti
Sojojin yankin Polisario na Morocco yayin fareti FAROUK BATICHE/AFP via Getty Images
Talla

Caccakar da fira Ministan Algeria AbdeAziz Djerad ke wa kasashen ketare na zuwa ne bayan da Amurka ta goyi bayan kasar Morrocco kan mallakar yankin na Polisario dake yammacin Sahara, bayanda Moroccon ta amince da maida huldar diflomasiya tsakaninta da Isra’ila.

Sai dai tuni mayakan na Polisario suka yi watsi da sanawar bazatan da shugaban Amurka mai baring ado Donald Trump ya yi, tare da shan alwashin cigaba da yakar dakarun Morocco har sai sun janye daga yankin na yammacin sahara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.