Morocco
Yan tawayen Polisario sun musanta sanarwar Morocco
Kungiyar yan Tawayen Polisario ta bayyana sanarwar Morocco na cewar zata janye jami’an ta daga yankin yammacin Sahara a matsayin yaudara.Sanarwar da kungiyar ta bayar ta ce janye dakarun Morocco daga Guerguerat ba zai haifar da komai ba, kuma yaudara ce ga kasashen duniya.
Wallafawa ranar:
Talla
Kungiyar ta ce har yanzu tana mutunta yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 1991 da kuma bukatar gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a dan baiwa yankin yancin cin gashin kan sa.
Morocco da kungiyar Polisario sun kwashe shekaru 17 suna gwabza yaki dan mallakar yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu